Digital Psychologist retweeted
10 INFECCIONES DE TRANSMISIÓN SEXUAL QUE TODO HOMBRE DEBERÍA CONOCER
1. la famosa Sifilis
1. Focus on improving yourself.
2. Stop checking her social media.
3. Don’t show your pain on social media.
Maza 6 da mata ke bi ba tare da sun roka ba.
Namijin da ya san darajarsa ba ya tilasta wa mace ta so shi. Yana nuna kulawa, amma idan ba a son shi, yana iya tafiya cikin mutunci.
1. Wanda ya san darajar kansa.
Kada ka mayar da mace ita ce tushen farin cikinka. Ka gina rayuwarka, domin farin cikinka bai kamata ya dogara akan samun mace ba.
2. Wanda baya roƙon soyayya.
Ka nuna kulawa, amma kada ka tilasta wa mutum ya so ka. Wanda yake sonka da gaske zai nuna maka hakan.
3. Wanda ya mayar da hankali kan ci gaban rayuwarsa.
Ka inganta rayuwarka, ka nemi kuɗi, ka cimma burinka. Kada neman mace ya zama babban aikinka.
4. Wanda ya daidaita ƙoƙarinsa da nata.
Idan kai kaɗai ne kake kira, aika saƙo da neman ganinta ko yaushe, ka ɗan ja baya ka ga ko ita ma za ta nuna hakan.
5. Wanda yake girmama lokacinsa.
Kada ka ajiye komai ko ka rinka katse aikinka duk lokacin da ta kira ka. Ka ci gaba da aikinka kana da burika.
6. Wanda baya riƙa neman tabbatar da cewa yana da daraja.
Ka kasance mai natsuwa wanda ya amince da kansa, ba tare da ka roƙi a so ka ba.
Ba wai yin wasan ɓoye-ɓoye ko nuna halin ko-in-kula ne yake sa a so ka ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka gina kanka, ka san darajarka, kuma kada ka rasa kanka saboda neman soyayyar wani.
#DigitalPsychologist
Abubuwa 5 da ke hana ka samun nasara.
1. Shagala akan abubuwan banza (abubuwa marasa amfani).
2. Tsoron fita daga inda ka saba (ka gwada wani abu).
Idan kana tsoron gwada sabon abu, ba za ka samu ci gaba ba.
3. Yawan jinkirta aiki.
Duk lokacin da ka ce sai gobe za ka yi abin da ya kamata ka yi yau, kana ƙara jinkirta nasararka.
4. Yin abubuwa da yawa lokaci guda.
Yawan tsallakawa daga wannan aiki zuwa wancan yana rage maka natsuwa da kwarewar aikinka.
5. Rashin jurewa/dagewa.
Ba za ka samu nasara ta hanyar yin abu yau gobe kuma ka bar shi na tsawon lokaci. Ka dage, ka yi aiki, domin ci gaba yana buƙatar lokaci.
#DigitalPsychologist
Babban Dalilin Da Yasa Bai Kamata Ka Tilasta Wani Abu Ya Faru Ba Shine Akwai Dalilin Rashin Faruwar.
#DigitalPsychologist
Abubuwa 5 Masu Firgitarwa Game da Halittar Dan Adam
1. Mutane da yawa a ɓoye suna jin daɗin wannan wahalar ko matsalar da kake fuskanta. Ba kowannensu ne yake son ganin ka ci gaba ba.
2. Za ka fi gane ainihin ma’anar kaɗaici ne ranar da abinda kake bawa mutane ya kare. Dayawa za su ɓace kamar basu sanka ba. Ka gina kanka kafin lokacin.
3. Wasu mutanen fatansu ganin ka faɗi, ko da kuwa ba ka taɓa yi musu wani laifi ba. Ba duk wanda ya san ka ba ne yake son ganin ka yi nasara.
4. Idan kana gina kanka mutane sunfi son suga ka gaza, maimakon su yarda cewa kana da baiwar da ta wuce tasu.
5. Mutane za su iya sauya mummunan halinsu akanka saboda ka shahara ko kuɗi. Ka gane cewa ba kowa ne yake sonka dagaske ba.
Ba kowa ne yake farin ciki da nasararka ba.
Kaine me ceton kanka a wannan rayuwar ba wani mutum ba.
Za mu sake haɗuwa...
Ka'idoji 7 dake nuna ka fara samun cigaba a rayuwa.
Nasara ba dole ne ta fara da bayyana a aljihunka ba. Wani lokacin tana bayyana ne a tunaninka, halinka, kamun kanka da yadda kake tafiyar da rayuwarka.
1. Ka daina yin masturbation (istimna'i) kuma daina kallonsa a matsayin mafita.
- Yanzu ka daina komawa gare shi duk lokacin da ka ji gajiya, damuwa ko kaɗaici. Kana fara koyon yadda za ka sarrafa lokacinka, hankalinka da sha’awarka, maimakon su mallake ka.
2. Kafi son zaman lafiya da kwanciyar hankalinka akan dangantakar da bata da anfani.
- Ka daina gardama da kowa, ka daina yawan bayanin kanka ga mutanen da ba sa son fahimtarka, kuma ka daina shiga duk wata hayaniya da ba ta da amfani.
3. Kana fara zama mutumin da ke son cigaba abin da ya sa gaba.
- Ba sai ka jira motivation ko ƙwarin gwiwa ba kafin ka yi abin da ya kamata ka yi.
4. Ka fara ɗaukar batun kuɗi da muhimmanci.
- Ka daina ƙoƙarin nuna wa mutane cewa kana da kuɗi, ka fara ƙoƙarin gina rayuwar da ba za ta dogara da nuna arziki ba. Kan fara neman ƙarin hanyar samun kuɗi, da sarrafa kashesu.
5. Ka fara ɗaukar lafiyarka da muhimmanci.
- Ka fara samun isasshen barci, motsa jiki, cin abinci mai kyau, da kula da abin da kake sakawa a jikinka. Kuma ka fahimci cewa jikin da kake rayuwa a cikinsa shi ne kayan aikinka na farko.
6. Ka daina neman amincewar kowa.
- Ba ka ƙara buƙatar kowa ya yaba maka ko ya amince da duk abin da kake yi ba. Kana samun kwanciyar hankali wajen yin abin da ka san ya dace da kai, ko da ba kowa zai fahimce ka ba.
7. Ka fara jin daɗin zama kai kaɗai.
- Ba ka buƙatar kullum a nishadantar da kai ko a ba ka kulawa. Kana iya zama kai kaɗai ba tare da jin kamar akwai wani abu da ka rasa ba. Ka fara zama abokin kanka.
8. Ka fara tunanin abin da zai amfani gobenka ba na jin dadin yanzu.
9. Kana murmurewa komai ya koma dai dai da sauri idan rayuwa ta buge ka.
- Matsalolin rayuwa suna cutar da kai, amma ba sa tarwatsa ka kamar yadda kake da. Kana koyo daga abin da ya faru, kana gyara kuskuranka, sannan ka sake tashi ka ci gaba.
10. Tun yanzu ka fara alfahari da kanka da kuma mutumin da kake zama.
- Rayuwarka ba ta zama cikakkiya ba tukuna. Amma kana iya kallon kanka ka ga bambanci tsakanin yadda ka kasance jiya da yadda kake yau.
Cin nasara ba iya lokacin da mutane suka fara ganin canjinka ba ne. Nasara tana farawa ne lokacin da kai da kanka ka fara ganin cewa ba ka ƙara zama daban.
Yanzu kana sarrafa kanka.
Yanzu kana gina kanka.
Yanzu kana daraja lokacinka.
Yanzu kana tunanin makomarka.
Yanzu ka fara zama mutumin da kake son zama.
Shekaru 2 sun isa dan uwa.... Zamu sake haduwa.
ABUBUWA 5 DA YA ZAMA DOLE KI SANI KAFIN AUREN KOWANNE NAMIJI.
Namijin 1 da ya dace ki aura, shi ne wanda yake da wadata, amma ba wai ta fuskar kuɗi ba.
1. Ki nemi wanda zuciyarsa take da wadatatuwar annuri (yawan farin ciki), wanda yake iya kawo farin ciki ko da lokacin rayuwa ta yi tsanani.
2. Ki nemi wanda yake da wadatatuwar Alkairi (kirki), wanda alherinsa ba ya dogara da abin da zai samu daga gare ki.
3. Ki nemi wanda yake da wadatatuwar soyayya (ƙauna), wanda zai so ki da gaske, ba iya lokacin jin daɗi kaɗai ba, har a lokacin kunci.
4. Ki nemi wanda yake da wadatatuwar juriya, wanda zai iya tsayawa da ƙafafunsa, ya zama mafaka idan rayuwarki zata girgiza.
5. Ki nemi wanda yake da wadata ta kamun kai, wanda yake iya sarrafa sha’awarsa, fushinsa da halayensa, ba wanda kowace zuciya za ta ja shi inda take so ba.
6. Ki nemi wanda yake da wadatatuwar tsoron Allah, domin dukiyar da ta fi kowace dukiya daraja ita ce zuciyar da ta san cewa Allah yana ganinta.
Ki sani... ainihin arzikin namiji ba ya cikin abin da ke aljihunsa ko banki. Yana cikin abin da yake cikin zuciyarsa, halinsa da mutuncinsa ne.
Kuɗi na iya gyara gida, amma hali ne ke zaunar da gida... Zamu sake haduwa.
#DigitalPsychologist
KA FAHIMCI YADDA KUƊI KE AIKI?
Ka fahimci yadda kudi ke aiki kuwa?
Ga abubuwa 5 da ya zama dole ka sani.
Ka koyi yadda kudi ke aiki kafin ka samesu.
1. YAWAN SAMUN KUƊI BA SHI NE ARZIKI BA.
- Kuma arziki ba wai yawan kuɗin da kake samu ba ne.
- Arziki shi ne abin da ka iya riƙewa, karewa da kuma ƙara haɓakawa daga cikin abin da kake samu.
Ba yawan abin da ke shigowa aljihunka ne ke gina maka wadata ba...
2. KOWACCE NAIRA YA KAMATA YA SAMU AIKI.
- Idan ba ka tsara wa kuɗinka inda zai je ba, to abubuwan da ba ka buƙata ne za su nema masa wurin zuwa.
- Ka daina barin kuɗinka ya tafi haka kawai ka nema masa aiki kafin ya kai kansa gurin da bai dace ba.
- Ka san nawa za ka kashe, nawa za ka ajiye, nawa za ka zuba jari, da kuma abin da za ka bari ya karu.
3. AJIYEWA TANA KARE KA SOSAI, ZUBA JARI KUMA YANA HAƁAKA KA.
- Ajiye kudi tana ba ka tsaro da kwanciyar hankali idan wani abu na gaggawa ya faru.
- Zuba jari kuma yana ba kuɗinka damar haɓaka da samar maka da ƙarin dukiya.
- Ba lallai ka zaɓi ɗaya ka bar ɗayan ba...
Kana buƙatar su duka.
4. YANAYIN HALAYENKA GA KUƊI SUN FI YAWAN ALBASHINKA TASIRI.
- Babban albashi ba zai iya gyara mugayen halayen kashe kuɗi ba.
- Idan kana samun kuɗi da yawa amma kana kashe su ba tare da tsari ba, yawan kuɗin da kake samu ba zai gina maka wadata ba.
- Ƙananan shawarwarin da kake yanke wa kanka a kowace rana ne, idan ka maimaita su na tsawon lokaci, suke gina maka dukiya.
5. KUƊI YANA SAYA MAKA 'YANCIN ZABAR ABU NE, BA FARIN CIKI BA.
- Manufar samun kuɗi ba wai ka mallaki abubuwa da yawa ba ne.
- Manufar ita ce ka samu ƙarin damar zaɓar irin rayuwar da kake son yi.
- Kuɗi ba su tabbatar maka da farin ciki... amma idan ka sarrafa su da hikima, za su iya ba ka ’yancin yanke shawarar abin da ya fi dacewa da rayuwarka.
6. CIGABAN KUƊI YANA FARAWA NE DA TSARI.
- Yawancin mutane ba suna rashin nasara bane saboda suna samun kuɗi kaɗan kawai.
- Sau da yawa, matsalar ita ce ba su da tsarin tafiyar da kuɗin nasu.
Ka san abin da ke shigowa.
Ka san abin da ke fita.
Ka san abin da za ka ajiye.
Ka san abin da za ka zuba jari.
Domin idan ba ka tsara wa kuɗinka hanya ba, kuɗin naka ne zai tsara maka rayuwa.
Ba yawan kuɗin da kake samu kaɗai ne ke nuna irin rayuwar da za ka yi ba.
Yadda kake sarrafa abin da kake samu shi ne ke nuna ko kuɗinka zai zama kayan jin daɗin ɗan lokaci ne... ko kuma tubalin gina makomarka.
Zamu sake haduwa....
Ɗaya daga cikin abubuwan da suke karya zuciyar namiji shi ne ganin wacce ka taɓa ba komai naka… ta zaɓi wani akan ka. Wadda ka taɓa mafarkin gina rayuwarka da ita.
Mutum zai tuna dararen da ya rasa bacci saboda ita. Kuɗin da ka kashe don faranta mata. Lokacin da ka manta da matsalolinka saboda ka tabbatar ita ɗin tana farin ciki.
Yanzu kuma gashi wani ne yake jin daɗin wannan kulawar da ka taɓa ba ta. Zaka gan ta tana murmushi da shi. Tana fitowa su hadu, tana farin ciki da wannan sabon mutumin.
Kai kuma kana nan kana ƙoƙarin fahimtar yadda makomar da kukayi kokarin gina mafarkinku tare ta zama tarihi.
Kuma abin da ya fi ciwo ma shi ne... Me yake da shi da ni ban samu ba? Na fishi komai.
Sai ka fara tunanin ashe yanzu duk shekarun da ka sadaukar mata don gina ta da faranta mata basu taɓa ba da wani ma’ana a wurinta ba.
Shawarata anan... kada ka yi gasa da shi.
Kada ka nemi bayani daga gare ta kan dalilin da ya sa ta zaɓe shi. Kada ka lalata kanka wajen ƙoƙarin tabbatar mata cewa ta yi kuskure. Ka bar su da rayuwarsu.
Kai ma kana da rayuwar da ke jiranka a gaba, iyalanka, tunaninka, lafiyarka da makomar da ka fara ginawa tun kafin ka saka ta a cikin mafarkinka.
Ina tabbatar maka ina kayi haka to wata rana za ka gan ta tare da wani… kuma zuciyarka ba abinda zataji. Ba za ka taba tuna ka taɓa sonta ba.
Abin da kuma zai kashe ka shi ne ka dakatar da rayuwarka saboda macen da ta ci gaba da rayuwarta da wani....
Zamu sake haduwa... INSHALLAH
Juma'at Mubarak ALPHA.
Idan ke mace ce kuma har yanzu ba ki taɓa bawa namiji kanki ba (yin jima’i) ba, ki sani cewa ba ki rasa komai ba. Akwai daraja a cikin mace wadda ta iya tsayawa kan abin da ta yarda da shi.
Idan rabuwa da budurwa ya sa rayuwarka ta tarwatse, to matsalar ba daga ita bane kadai, wataƙila ka ba ta matsayi ne fiye da wanda ya kamata ta samu a rayuwarka.
Look! Abinda ko yaushe ake fada maka shine kaso kanka, kada son wani abu yasa ka manta da naka mafarkan na rayuwa.
Ka mai da ita wani abin daban.
Ka bata abin da ya kamata ya kasance naka, burinka, rayuwarka da makomarka.
A yanzu babban burinka kada kawai ya zama mantawa da ita. A'a ka hada da gina rayuwar da ba za ta tsaya ba saboda wata ta tafi.
Ka gyara tunaninka.
Ka nemi abin da kake son cimmawa.
Ka gina sana’arka, aikinka da makomarka.
Ka nemi kuɗi sosai.
Idan soyayya ta zo, sai dai ta ƙara wa rayuwarka armashi. Amma kada ka mayar da mace ita ce manufar rayuwarka.
Mace ta kasance wani ɓangare na tafiyarka kawai, karta zama ita ce inda tafiyar zata ƙare..
Idan da gaske kana son zama namijin da yake rayuwa da manufa, ba wanda shaawa ke jansa duk inda ta ga dama ba, to fara gina abubuwan da rabuwa, ƙin amincewa, ko tafiyar wata mace da za ta iya kwace maka.
Ka gina kanka har rayuwarka ta zama tana da daraja ko da babu wanda yake tare da kai.
Abin da ya kamata ka rasa saboda rabuwar soyayya ba kanka ba ne.
Ka rasa kowacce mace idan dole ne, amma kada ka rasa rayuwarka saboda ita.
Rashin sanin ilimin zama da mace hukuncin ɗaurin rai da rai ne akan namiji.
Mace idan tana soyayya, abin yana da kyau a gani.
Zatayi murmushi duk lokacin da take kallon wayarta.
Tana saka kyawawan status a shafinta.
Tana jin daɗin komai har abin shan da take sha mai sanyi.
Tana rayuwarta irin ta yarinyar da zuciyarta babu komai sai farin ciki, Masha Allah.
Amma namiji idan ya kamu da soyayya?
Lamarin ya kan zama daban.
Namijin da a da yake da cikakken iko da rayuwarsa, kwatsam sai ya fara yanke shawara bisa ga yadda wata mace tace, koma bata kula shi.
Ta ce tana son ganinsa?
Sai ya soke duk wani shirin da yake da shi da aikin da yake yi.
Ta ce tana son wani abu mai tsada?
Sai ya manta da asusun da yakeyi na ɗan lokaci.
Namijin da a da yake ƙirga kowanne irin kuɗin da zai kashe, kwatsam sai ya fara kashe kuɗi kamar wanda ya manta da nauyin rayuwarsa dana iyayensa.
Abokansa za su daina ganinsa kamar da.
Komai zai fara raguwa.
Burinsa na rayuwa mai kyau ya fara komawa baya.
Amma shi har yanzu yana ganin abin da yake yi daidai ne, saboda kawai ya ce yana soyayya.
Sai wata rana, sai ta fara nesanta kanta da shi.
Yanzu kuma sai ya koma kallon wayarsa ba kakkautawa yana jiran sakonni.
Yana nazarin kowanne saƙo da ta turo.
Yana tambayar kansa me ya canza.
Yana ɗorawa kansa laifi.
Yana tunanin yadda zai dawo da kulawar da yake samu a da, ba tare da ya roƙe ta ba.
Ya da kyau Namiji iya ƙaunar mace sosai da zuciya ɗaya, amma ba tare da ya rasa kansa ba.
Nauyin da ke kansa yana nan.
Burinsa yana nan.
Ƙa'idodinsa suna nan.
Samun mace a rayuwarsa bai kamata ya kawar da waɗannan abubuwa ba.
Mace za ta iya zama ɓangare na rayuwarka.
Amma da zarar ka mai da ita duniyarka,
za ka fara sakaci da ainihin mutumin da ta fara sha'awa tace tanaso a farko.
Ka ƙaunace ta.
Ka kula da ita.
Amma kada ka yi watsi da kanka saboda soyayya.
Mata zasu lalata rayuwarka idan baka fahimcesu ba.
Kana da ’yancin zaɓar duk Macen da kakeso, amma ba ka da ’yancin guje wa sakamakon zaɓinka.
Kada ka raina, ko ka yi wa radadin da ba ka taɓa fuskanta ba ba’a.
Manufar ita ce ka gina rayuwa da ba za ta rushe ba don kawai saboda wani ya bar ka.
Idan an zo bangaren mu’amala da mutane, ka rage tsammaninka a kansu.
Idan mutum baka da ma’aunin ɗabi’a da zai jagorance ka, hankalinka zai iya ba ka hujjar aikata komai.
Me zai sa in ɓata lokacinka, alhali lokacinka shi ma lokaci na ne? Ai tare muke batawa...
Ka tabbatar mutanen da kake more rayuwa tare da su su ne waɗanda za su zo su cece ka idan ka shiga matsala.
Ka yi hattara da amincin mutumin da bai taɓa fuskantar jarabawar kuɗi ko tsoro ba, ba ka san yadda zai kasance ba idan an gwada shi.
A lokacin da sunanka ya zama mafita ga matsalar wani, ka sani ka kai wani babban matsayi na rayuwa.
Matukar kana raye, babu wata rashin nasara da ta ƙare, mafi yawan cin kaso yana farawa ne a cikin tunanin mutum.
Babu wani dalili da zai sa ka zama mai neman faranta wa kowa rai, domin mutane ba sa taɓa gamsuwa gaba ɗaya.
Ko a mafi kyawun ranakunmu, har yanzu mu masu zunubi ne, waɗanda Allah Ya ceta da rahamarsa.
Na duba cikin ƙoƙonka ne domin in ga ko kana buƙatar ƙari, kai kuma ka duba cikin nawa ne domin ka ga ko abin da nake da shi ya fi naka. Ba daga muke ba...
Wasu mutanen suna nuna kamar sun damu da kai ne, alhali abin da suke nema kawai shi ne su tona asirin rayuwarka.
Kurakuranka da aibunka na iya zama cikakken abin da zuciyar mutumin da aka ƙaddara ya ƙaunace ka take nema, domin dashi ne ake ruguza ka.
SAƘO GA DUK WADANDA BA SU DAMU BA. Za ku damu idan abin ya faru a kanku.
Ina mamakin.... ina tunani yake zuwa idan an manta da shi?
Ci gaba da rayuwarka kamar ba ka taɓa saninsu ba, domin Gaskiyar shine, wataƙila ba ka taɓa sanin ainihin su ba ne yasa ka yadda dasu.
Shekaru goma daga yau.... wannan abin da yake damunka a yanzu zai kasance yana da muhimmanci?
Mata zasu rushe ka idan baka fahimcesu ba..
Juma'at Mubarak... Zamu sake haduwa.









