
Founder, @NovaAcademy01 | Our Vision Is to Build the Future of Blockchain & Web3 Education for Our Community.
Nigeria
Joined June 2020
- Tweets213
- Following28
- Followers354
- Likes447
Sadiq Jega retweeted
SANARWAR NEMAN ƘWARARRUN MALAMAI (PHYSICAL CLASS) – ABUJA
NovaChain Academy na sanar da buɗe guraben neman ƙwararrun malamai da masana a fannoni daban-daban na fasahar zamani, domin ƙarfafa tawagar koyarwa ta Academy a Abuja.
Ana neman ƙwararru a fannoni kamar haka:
1. Blockchain and Cryptocurrency
2. Web3 Development
3. Digital Security
4. Artificial Intelligence (AI)
1. WURIN AIKI
Abuja, Najeriya.
2. LOKACIN DA YADDA ZA A RIƘA KOYARWA
Waɗanda za su samu guraben aikin za su riƙa koyarwa da jagorantar ɗalibai kai tsaye a cikin aji (Physical Classes) a Abuja, daga Litinin zuwa Juma'a.
3. SHARUƊƊAN NEMA
Masu neman wannan aiki dole ne su cika waɗannan sharuɗɗa:
1. Kasancewa masu cikakken ilimi da ƙwarewar aiki a fannin da suke son koyarwa.
2. Samun ƙwarewar koyarwa da iya jagorantar ɗalibai.
3. Iya sauƙaƙa darussa masu sarkakiya na fasahar zamani domin ɗalibai su fahimce su cikin sauƙi.
4. Iya koyarwa da sadarwa da ɗalibai cikin harsunan Turanci da Hausa.
4. YADDA ZA A NEMA
Duk masu sha'awar wannan aiki waɗanda suka cika sharuɗɗan da aka gindaya, su aika da waɗannan bayanai zuwa adireshin imel na hukuma na Academy:
1. Cikakken suna.
2. Fannin da suke da ƙwarewa a cikinsa.
3. Takaitaccen bayani kan ƙwarewarsu da gogewar aikinsu.
4. Lambar waya.
5. Yankin da mutum yake zaune a Abuja.
5. ADIRESHIN IMEL NA AIKAWA
[email protected]
Za a fara neman aikin daga yau, 25 ga November, inda za a rufe ranar 30 ga November 2026.
Bayan kammala karɓar buƙatun, Academy za ta tantance dukkan masu neman aikin tare da tuntuɓar waɗanda suka cancanta domin mataki na gaba.
ISSUED BY:
NOVACHAIN ACADEMY
25th November, 2026.
Sadiq Jega retweeted
Assalamu Alaikum Warahmatullah.
Muna taya mutum 2,500 da suka samu tallafin karatu murna.
Idan ka san kana cikin waɗanda suka cike fom ɗin neman tallafin karatu wanda Minista Bello Matawalle ya ɗauki nauyinsa, to duk wanda yake da rabo an tura masa saƙo kai tsaye cikin wayarsa. Ka shiga message da ke cikin wayarka ka duba. Idan kaga sako, ka yi ƙoƙarin yin magana a lambar da aka tura maka domin a saka ka cikin Class.
Sannan, kasancewar sama da mutum 4,000 ne suka nemi tallafin, Founder na wannan Academy ya nemi alfarma domin a ƙara yawan waɗanda za su amfana. Inda daga mutum 1,000 da Minister ya ɗauki nauyin karatunsu, Minister ya ƙara bada damar mayar da adadin mutanen zuwa 2,500.
Don haka, yanzu haka an tura ma mutum 2,500 sako, muna taya waɗanda suka samu murna. Waɗanda ba su samu ba kuwa, muna roƙon Allah Ya kawo wata dama da za su amfana.
NovaChain Academy
23/11/2026
Sadiq Jega retweeted
Banbancin Forex, Crypto da DEX: A Sauƙaƙe 💱
Mutane da yawa na haɗa waɗannan abubuwa uku, alhali kowanne daban yake. Ga bayani a takaice:
1. Forex 🌍
Forex shi ne ciniki da kuɗaɗen ƙasashe, misali Dollar, Pound, Euro ko Naira. Kana saye ɗaya, ka sayar da ɗaya, kana neman riba daga canjin farashinsu.
📌 Misali: Ka saya Dollar a farashi mai ƙaranci, ka sayar idan ya tashi.
🏦 Bankuna, gwamnatoci da manyan kamfanoni ne ke da iko a cikinsa. Ana yin sa ta hannun broker.
2. Crypto 🪙
Crypto kuɗi ne na dijital da ke tafiya a kan fasahar *blockchain*, kamar Bitcoin, Ethereum da Solana. Babu banki ko gwamnati da ke mallakarsa.
📌 Ana iya saye, riƙewa, aikawa ko amfani da shi wajen biyan kuɗi da ayyukan fasaha.
⚡ Farashinsa na tashi da faɗuwa da sauri fiye da kuɗin ƙasa.
3. DEX 🔄
DEX (Decentralized Exchange) ba wani kuɗi ba ne, wuri ne na cinikin crypto. Babu kamfani ko ma'aikaci a tsakani, ana yin cinikin kai tsaye ta hanyar smart contract daga wallet ɗinka.
📌 Misali: Uniswap, PancakeSwap.
🔑 Kai kake riƙe kuɗinka (wallet ɗinka), amma kai ne kuma da alhakin tsaronsa. Idan ka rasa seed phrase, ka rasa kuɗinka.
🧠 A taƙaice:
- Forex: ciniki da kuɗin ƙasashe
- Crypto: kuɗin dijital na blockchain
- DEX: wurin cinikin crypto ba tare da tsaka-tsaki ba
⚠️ Gargaɗi:
Duka ukun suna da haɗari. Kada ka saka kuɗin da ba za ka iya rasawa ba. Ka fara koyo kafin ka fara ciniki, kuma ka yi hattara da masu yaudara da ke alƙawarin riba mai sauri.
💡 Ka tuna: ilimi shi ne jari na farko.
Wanne ne a cikinsu ka fi so ka ƙara fahimta? Rubuta a comment! 👇
Wannan ilimi ne kawai, ba shawarar kasuwanci ba
#NovaChainAcademy #Forex #Crypto #DEX #Fasaha #Matasa
Sadiq Jega retweeted
SANARWA TA MUSAMMAN GA MATASAN NIGERIA
Ministan Tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya ɗauki nauyin horas da matasa ’yan Najeriya guda 1,000 a fannin fasahar Blockchain da Web3, domin ba su damar fahimtar wannan sabuwar fasaha tare da amfani da ita wajen samar wa kansu da sauran al’umma hanyoyin dogaro da kai.
Za a gudanar da wannan horaswa ne na tsawon watanni biyu (2) kacal, ta hanyar yanar gizo (Online), domin bai wa matasa daga sassa daban-daban damar cin gajiyar wannan shiri.
Saboda haka, duk wanda yake da sha’awar cin gajiyar wannan dama, yana iya cike fom ɗin neman shiga shirin. Idan Allah Ya ba ka sa’a, za ka kasance cikin matasa 1,000 da za su amfana da wannan tallafi.
Jadawalin Shirin:
- 15 ga Nuwamba, 2026: Fara karɓar fom ɗin neman shiga.
- 20 ga Nuwamba, 2026: Rufe karɓar fom.
- 21–27 ga Nuwamba, 2026: Tantance masu neman shiga da zaɓen waɗanda suka cancanta.
- 1 ga Disamba, 2026: Fara karatun horaswa, Insha Allah.
Muna kira ga matasa masu sha’awar fasahar zamani da su yi amfani da wannan dama wajen haɓaka iliminsu, ƙwarewarsu da kuma samar wa kansu makomar dogaro da kai, Sannan wnada yasan bayada lokacin tsayawa ya koya don Allah kada ya tare gurbin da wani zai iya amfarsa a rayuwa.
Kada ka bari wannan dama ta wuce ka!
Ga hanyar cike fom ɗin neman shiga: docs.google.com/forms/d/e/1F…
NovaChain Academy
15/11/2026
Alhamdulillah
SANARWA | NOVACHAIN ACADEMY
Alhamdulillah, mun kammala aikin tantancewa da zaɓen ƙwararrun malamai da za su kasance cikin tawagar koyarwa ta NovaChain Academy.
A cikin mutane 13 da aka tantance domin koyar da darussan Academy, mutane 6 ne suka samu nasarar cika ƙa’idoji da buƙatun da muka gindaya, tare da dacewa da muradun NovaChain Academy na samar da ingantaccen ilimi da ƙwarewa.
Bisa wannan cancanta, an ba su Appointment Letters domin fara aikin koyarwa a NovaChain Academy.
Za su kasance suna koyar da fannoni daban-daban da suka haɗa da:
• Blockchain Technology
• Web3 Development
• Smart Contracts
• Decentralized Applications (DApps)
• Digital Assets
• Decentralized Finance (DeFi)
• Tokenomics
• Artificial Intelligence (AI)
• Digital Security
• Remote Work & Digital Entrepreneurship
Wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen NovaChain Academy na tabbatar da cewa ɗalibai sun samu ƙwararrun malamai, ingantaccen ilimi, da tsarin koyarwa mai ma’ana.
Muna taya sabbin malamanmu murna, tare da fatan Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da aka ɗora musu cikin nasara.
NOVACHAIN ACADEMY
Africa’s Hub for Blockchain & Web3 Education
29/09/2026
Sadiq Jega retweeted
JIRA YA ƘARE — SAURA KWANA UKU A RUFE REGISTRATION!
Muna sanar da duk waɗanda suke shirin shiga NovaChain Academy cewa za a rufe Registration ranar 28 ga Satumba, 2026 — wato yau saura kwana uku kacal!, Wannan ita ce damar ku ta ƙarshe kafin a rufe rajista.
Domin amfana da samuwar fasahar Blockchain wajen inganta kasuwanci da sauran abubuwan da suka shafi rayuwarmu, bai kamata a duk lokacin da sabon abu ya zo a duniya, al’ummarmu su kasance suna bari ana barin su a baya ba.
Insha Allah, ga waɗanda suka kasance tare da mu, muna musu albishir da cewa mun tanadar musu da malamai waɗanda suke da cikakkiyar ƙwarewa a fannoni daban-daban.
Ku yi ƙoƙarin kasancewa cikin ɗalibanmu na farko waɗanda za su fara wannan sabon tafiya tare da NovaChain Academy.
💰 KUƊIN REGISTRATION: ₦10,000
🏦 GTBank:
3005358753
NOVACHAIN ACADEMY LTD
🏦 Moniepoint:
6999531401
NOVACHAIN ACADEMY LTD
⚠️ MUHIMMI: Kafin ku yi biyan kuɗi, ku tabbatar cewa sunan asusun da ya bayyana shi ne NOVACHAIN ACADEMY LTD.
📲 BAYAN BIYAN KUƊI:
A tura receipt ta WhatsApp zuwa:
07069591722
☎️ ƘARIN BAYANI:
09135800666
⏳ KADA KA JIRA GOBE!
Yi Registration ɗinka yanzu domin ka samu damar kasancewa cikin ɗaliban da za su fara karatu a 01/10/2026.
📢 Domin ganin ayyukanmu da samun ƙarin bayani, ku shiga Official Channel ɗinmu:
t.me/NovaChainBA
NOVACHAIN ACADEMY
📅 25/09/2026
Sadiq Jega retweeted
WATA BIYU KACAL DA FARA TAFIYA! SHIN KUN SAN ABIN DA NOVACHAIN ACADEMY TA CIMMA?
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!
Babu abin da zamu iya cewa ga Allah (SWT) bayan godiya a kan wannan babbar ni'ima da Ya yi mana ta samun gagarumar nasara cikin watanni biyu kacal da fara tafiyar NovaChain Academy, A cikin wannan ɗan ƙaramin lokaci, mun samu damar aiwatar da abubuwa da dama waɗanda suka ƙara tabbatar mana da cewa tafiyar da muka fara tana da muhimmanci kuma tana da tasiri a cikin al'umma.
GAYYATAR MASANA DA MASU KWAREWA
Daga cikin abubuwan da muka gabatar a cikin waɗannan watanni biyu, mun gayyaci masana da ƙwararru daban-daban domin su zo su raba iliminsu da ƙwarewarsu tare da community ɗinmu, musamman a fannonin Web3, Blockchain da sauran fasahohin zamani.
Daga cikin waɗanda muka gayyata akwai:
- Mahmud Galadanci
- Sanusi Danjuma Ali
- Aliyu Samba
- Barr. Abdullahi-Hadee Isah Ibrahim
- Aliyu Dahiru Aliyu
- Ahmad XM, wanda wani uzuri ya hana shi samun damar halartar shirin.
Muna matuƙar godiya ga dukkan waɗannan ƙwararru bisa lokacin da suka ba mu da kuma ilimin da suka zo suka raba tare da al'ummar NovaChain Academy. Hakika, al'umma ta amfana da gwala-gwalan ilimi daga gare su.
GOYON BAYAN AL'UMMAR CRYPTO
Haka kuma, mun samu gagarumin goyon baya daga ƴan Crypto, manya da ƙanana, waɗanda duk da cewa ba sa cikin shirin karatunmu kai tsaye, sun taimaka mana ta fannoni daban-daban bayan sun fahimci manufar da muke da ita da kuma irin sauyin da muke son samarwa a Arewacin Najeriya.
Daga cikin waɗanda suka ba mu goyon baya akwai:
Chizo1germany, Rabi'u Biyo, Engr. Bakaka, Imamu Sheka da sauran waɗanda suka taimaka mana ta hanyoyi daban-daban, Muna matuƙar godiya gare su, kuma muna addu'ar Allah Ya saka musu da alheri.
ƘARUWAR YARDA DA TASIRIN NOVACHAIN A CIKIN AL'UMMA
Alhamdulillah, muna ganin yadda mutane suke ƙara fahimtar manufar NovaChain Academy da kuma muhimmancin ilimin da muka zo da shi, Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara tabbatar mana da hakan shi ne yadda muka samu ɗimbin mutane suka yi registration domin fara karatunmu a ranar 1 ga Oktoba, 2026, duk da cewa tafiyar Academy ɗinmu ba ta wuce watanni biyu ba, wanda har yanzu ana ci gaba da samun sababbin masu registration.
Haka kuma, yadda social media platforms ɗinmu suka samu ɗimbin mabiya cikin wannan ɗan ƙaramin lokaci ya ƙara tabbatar mana da cewa saƙonmu yana isa ga al'umma, kuma akwai mutane masu sha'awar samun ingantaccen ilimi a fannonin da muka mayar da hankali a kansu.
COMMUNITY ƊINMU A SOCIAL MEDIA
1. Facebook: muna da Mabiya 10,990 Link: facebook.com/share/1EQhfQ9FL…
2. Telegram Channel: Muna da Mabiya 4,292 Link: t.me/NovaChainBA
3. WhatsApp Channel: Muna da Mabiya 2,478 Link: whatsapp.com/channel/0029Vb8…
4. X (Twitter): Muna da Mabiya 1,364 Link: nitter.gq/NovaAcademy01
MENENE MAKOMAR NOVACHAIN A SHEKARU BIYU MASU ZUWA?
Idan Allah Ya nuna mana wannan irin nasara cikin watanni biyu kacal, to muna kallon shekaru biyu masu zuwa da kyakkyawan fata da kuma babban buri, Insha Allah akwai gagarumar tafiya a gabanmu, Ba mu san irin girman abin da Allah zai kai mu gare shi ba, amma muna da yakinin cewa idan muka ci gaba da aiki da gaskiya, jajircewa, ilimi da kyakkyawar niyya, za mu iya ganin abubuwa masu girma a nan gaba.
Babban burinmu shi ne Allah Ya karɓi niyyarmu, Ya taimake mu wajan cimma manufarmu, Ya sanya wannan tafiya ta zama sanadin amfani ga al'umma, musamman wajan bunƙasa ilimi da ƙwarewar matasa a fannonin fasahohin zamani, Fatanmu shine kada Allah Ya bar mu da ƙarfin kanmu. Ya duba niyyarmu da manufar da muke da ita ga al'ummarmu, Ya ba mu hikima, ƙarfin guiwa da ikon sauke amanar da muka ɗauka.
Muna ƙara mika godiyarmu ga Allah (SWT), sannan muna miƙa saƙon godiya ga dukkan ɗalibai, mabiya, malamai, masana, masu ba da shawara, masu goyon baya da duk wanda ya kasance wani ɓangare na wannan tafiya, Muna kuma neman ƙarin Addu'a daga gare ku.
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu.
NOVACHAIN ACADEMY
22/09/2026
Sadiq Jega retweeted
SANARWA!!! 📢
MUNA NEMAN ƘARIN ƘWARARRUN MALAMAI.
NovaChain Academy na sanar da buɗe guraben aiki ga malamai ƙwararru a fannin Blockchain, Web3 Artificial Intelligence (AI), Digital Security, Remote Work & Digital, domin koyarwa da horas da ɗalibanmu, Muna neman mutane masu ilimi, ƙwarewa, gogewa da kishin koyarwa, waɗanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajan gina ƙwararrun matasa da kuma haɓaka ilimin fasahar zamani a cikin al’umma.
SHARUƊƊAN AIKIN.
Zamu ɗauki waɗanda suka cancanta aiki na tsawon watanni shida (6) a matsayin Contract Staff, A yayin wannan wa’adin, ma’aikaci zai kasance yana samun albashi kowane wata bisa tsarin aikin da aka amince da shi, Bayan kammala wa’adin watanni shida, idan ma’aikaci ya nuna ƙwarewa, jajircewa, ingantaccen aiki da cikakkiyar cancanta, NovaChain Academy na iya ba shi damar ci gaba da aiki a matsayin Permanent Staff.
Sabbin malaman da za a ɗauka za su yi aiki tare da ƙwararrun malaman da muke da su a yanzu, domin samar da ingantaccen tsarin koyarwa, musayar ilimi da haɗin gwiwa, Muna son bayyana cewa tunaninmu ba zai tsaya ga malaman da muke da su yanzu kawai ba, Saboda akwai wasu lokuta da malami zai iya samun uzuri ko wasu dalilai da za su hana shi ci gaba da aiki, muna son gina ƙungiyar malamai mai ƙarfi da faɗi, wadda za ta bai wa ƙwararru dama a kowane lokaci.
A NovaChain Academy, muna ba da dama ne bisa:
✅ Cancanta
✅ Ilimi
✅ Ƙwarewa
✅ Gogewa
✅ Jajircewa da ƙwazo
Ko wanene kai, daga ina ka fito, ko wane matsayi kake da shi a yanzu—idan kana da cancantar aikin, za mu yi la’akari da kai, Ba za mu ɗauki mutum aiki saboda suna, matsayi ko sanayya ba, Cancanta da ƙwarewa su ne ginshiƙan zaɓinmu.
📩 YADDA ZA KA NEMA
Idan kana da sha’awar wannan gurbi kuma ka yi imanin cewa ka cancanta da aikin, turo mana da.
🔹 Cikakken suna
🔹 Fannin da ka ƙware a kai
🔹 Takaitaccen bayani kan ƙwarewarka da gogewarka
🔹 Lambar wayarka
📧 Email:
[email protected]
Za mu duba bayanan duk masu neman aikin, sannan mu tuntubi waɗanda suka dace da buƙatun aikin.
Muna neman ƙwararru.
Muna gina ƙwararru.
Muna shirya ɗalibanmu domin makomar fasahar zamani.
NovaChain Academy
16/09/2026
BANA BA KU SHAWARAR SAKA HANNUN JARI A KAMFANIN DANGOTE.
Tun lokacin da aka fara wannan maganar wasu mutane ke yawan tambaya ta akan yadda abin yake, Jiya ma wani ya ce in koya masa yadda ake saka hannun jari, kasancewar ina jin nauyinsa, yasa na ƙara bincike a kansa har na fahimci abin da ya kamata in sani daga ciki Wanda kuma na zaɓi wannan hanya domin ba da shawara ga talakawa ire-iren na, domin wasu abin da suke tunani shi ne dare ɗaya za su yi kuɗi tun da sun saka hannun jari a kamfanin mafi arzikin kuɗi a Afirka😁
Bari in ba ku misali na hankali, talaka irina, wani zai iya qalula ya saka 500k hannun jari. Misali, a ɗauki shekaru goma, sai kamfanin Dangote ya ninka sau biyar Ni da na saka 500k, kuɗina sun koma 2.5m. Shi kuma Mai Girma Dangote, kuɗinsa daga 54.81 tiriliyan sun koma 274.05 tiriliyan. Anan, waye ya ci riba? Amsa: Dangote, yayinda ni talaka na ɓata wa kaina lokaci.
Miyasa nace na ɓata wa kaina lokaci? Duk matashin da yake da jarin 500k ya tsaya ya yi abin da ya kamata a kasuwa yadda ya kamata, tare da addu’a, cikin shekaru 10 kada ka yi mamakin jarinsa zai haura 20m ko 30m. Ina ba da misali ne best of experience da nake da shi a kasuwancin da nake yi tsakanin Ghana da Nigeria.
Nasan wani zai iya cewa to ai akwai ƙalubale, kuma komai zai iya faruwa. Haka ma a kamfanin Dangote akwai ƙalubale, domin kamar yadda kake tunanin riba, haka dole ka yi tunanin asara, domin kasuwanci ne ake. Sannan wani zai iya cewa ai kamfanin zai iya haura haka. Eh, kuma zai iya ƙasa da haka, domin na yi wannan hasashe ne bisa dogaro da kamfaninsa na Cement, wanda daga lokacin da aka fara saka hannun jari zuwa yau shekaru 16 kenan, amma waɗanda suka saka hannun jari dukiyarsu ta haura sau bakwai.
Wanda ya saka jarin 500k a kamfanin sa na siminti yanzu kuɗinsa sun koma 3.5m, Wanda in kasuwanci ne ake tsawon shekaru 16, maganar maza kuɗi za'ayi Wallahi, Malam Masu jarin 500k shekarau 16 da suka wuce Allah kaɗai ya san Yanzu ko mutane nawa suka shiga cikin jerin masu kuɗin gaske, waɗanda yanzu wasu daga cikinsu suna da yara a ƙarƙashinsu da suka fi ƙarfin 3.5m. Wasu ma ina da yakinin za su iya kyautar da 3.5m ba su ji komai ba, saboda tsabar albarkar da kasuwancinsu ya yi cikin shekaru 16.
Abin da nake son cewa a nan shi ne, wannan harka ba abin dogaro ba ce ga talaka wanda yake neman gina rayuwarsa. Harka ce da aka buɗe wa barayin ƴan siyasa da kuma masu kuɗi, waɗanda rayuwarsu a gina take, suna da hanyoyin samun kuɗi ba ɗaya ba, ba biyu ba. Suna da kuɗi ajiye a banki, sun rasa yadda za su dasu, sai su yanke shawarar bari su saka, da kuɗinsa su yi zaman banza a Account. 😁 Shi ne Uncle Dangote ya fake da taimakon talakawa, amma haƙiƙanin gaskiya, masu kuɗi da ƴan siyasa aka buɗe wa wannan business.
Wani zai ce, Ai Baban Fa’eez, ban iya kasuwa ba, kuma ban san hanyar Ghana ba. To, ai ni ma ba da sani hanyar Ghana aka haife ni ba. Shi ma Dangote, hanyoyin da ya yi nasara a kansu ba da su aka haife shi ba. Tashi ya yi, Allah ya taimake shi. Don haka kai ma tashi za ka yi, ka nemo hanyoyi ka taimaki kanka, ba ka yi kwance kana jiran wani ya nemo maka nasarar gobenka ba. Wannan tunanina ne da fahimta na, kuma babban abin da nake son isar wa ga ƴan uwana matasa shi ne kada ku kashe zuciyarku a kan wannan hanya ta Dangote, domin wallahi 99.9% Dangote, barayin ƴan siyasa da masu kuɗi ya taimaka a wannan hanya, ba talaka mai jin yunwa ba, indai kai talaka ne koda 50k zaka saka indai Kanada kwarewa a wata sana'a wallahi gwara ka kaita can da ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi, wannan abin koda talaka bai saka hannun jari ba waɗanda akayi domin su zasu cike gurbin da yake buƙata😁
Idan taimakon mu zaiyi wanda kowa zai amfana ya rage farashi suga shinkafa da sauran abubuwan da talaka ke buƙata kullum domin ya rayu amma wannan hanya babu inda aka taimaki talaka Maganar gaskiya kenan.
Baban Ahmad Fa’eez
15/09/2026
1
7
207
Sadiq Jega retweeted
A yau za mu tattauna yadda NovaChain Academy za ta gina tsarin karatu daga Beginner zuwa Advanced, tare da discipline, research, teamwork, assignments da practical Web3 skills.
🎯 Manufa: Gina ɗalibai masu ilimi, skills da damar bayar da gudummawa a Web3 ecosystem.
🚀 Building Web3 Knowledge, Skills & Contributors.
Join Now👇
t.me/NovaChainBA
Sadiq Jega retweeted
🚀 NOVACHAIN ACADEMY X SPACE
🎙️ Topic:
“NovaChain Academy Learning System: Tsari, Discipline & Web3 Growth”
A wannan X Space za mu tattauna yadda NovaChain Academy za ta gina ingantaccen tsarin karatu da zai taimaka wa ɗalibai su fahimci Web3 daga Beginner zuwa Advanced, tare da samun practical skills.
Za mu mayar da hankali kan:
🔹 Structured Learning
🔹 Discipline & Consistency
🔹 Research & Self-Learning
🔹 Assignments & Practical Tasks
🔹 Teamwork & Discussion
🔹 Web3 News & Industry Awareness
🔹 Assessment & Progress Tracking
🔹 Practical Web3 Skills
Manufarmu ba ita ce koyar da Web3 ta hanyar lectures kawai ba. Muna son gina ɗalibai masu ilimi, discipline, practical skills, research ability da damar bayar da gudummawa a Web3 ecosystem.
NovaChain Academy
Join Now👇
t.me/NovaChainBA
Building Web3 Knowledge, Skills & Contributors. 🚀
Masha Allab❤
SHIRYE-SHIRYEN FARA KARATU SUN KUSA KAMMALA!
⏳ Lokacin rufe rajista ma ya kusa ƙarewa!
Alhamdulillah, shirye-shiryen fara karatu a NovaChain Academy sun yi nisa sosai. A yanzu, abubuwa biyu ne suka rage mana:
🌐 1. Cikakken Website na Academy Muna kan hanyar kammala gina babban website ɗin Academy, musamman ganin cewa mun yi rajista da National Board for Technical Education (NBTE), Abuja, ƙarƙashin Ministry of Education. Website ɗin zai kasance ɗaya daga cikin hanyoyin da za a iya ganin tsarin koyarwa da ayyukan Academy.
🎓 2. Adadin Ɗalibai
Mun riga mun kayyade adadin ɗaliban da Academy za ta iya ɗauka tare da kula da su yadda ya kamata na tsawon watanni shida. Da zarar adadin ya cika, rajista za ta tsaya kuma bazamu kara daukan dalibai ba har sai bayan watanni shida, idan Allah Ya kaimu.
ME YASA YA KAMATA KA SHIGA NOVACHAIN ACADEMY?
Kada ka yi tunanin cewa wannan Academy ta masu Crypto kaɗai ba ce. ❌
Ko da ba ka cikin duniyar Crypto, akwai abubuwa da dama da za ka iya amfana da su, Blockchain, Web3, AI, DeFi da sauran sabbin fasahohi suna sauya yadda duniya ke aiki. Fahimtar waɗannan fasahohin na ƙara zama muhimmi sosai a wannan zamani da muke ciki.
Wannan ƙarni ne na fasaha. Idan kana da burin ƙara iliminka, koyon sabbin fasahohi, fahimtar Blockchain da Web3, ko kuma shirya kanka domin damar da ke kunno kai a duniyar dijital, wannan ita ce damar ka.
A baya, mun tattauna da ƙwararru da masana kan Blockchain, Web3, Cybersecurity da sauran fasahohin zamani. Daga cikin waɗanda muka tattauna da su akwai Barr. Abdul-Hadee Sunusi, Danjuma Ali, Aliyu Dahiru Aliyu, Aliyu Samba, da kuma Mahmud Galanci, wanda ƙwararre ne a fannin Cybersecurity, da sauran masana.
🎙️ Kuna iya shiga cikin Channel ɗinmu na Telegram domin sauraron bayanan murya (Audio) na waɗannan muhimman tattaunawa da maudu’ai da masana suka gabatar, tare da sauran abubuwan da muka gabatar a baya, ta hanyar wannan link: t.me/NovaChainBA
🔔 RAJISTA HAR YANZU BA TA RUFE BA!
Idan kana da niyyar shiga, ka gaggauta kammala rajistarka kafin wuraren da aka tanada su cika.
💳 HANYAR BIYA
GTBank: 3005358753
NOVACHAIN ACADEMY LTD
OPay: 7069591722
NANA ISAH
⚠️ MUHIMMI BAYANI: Kafin ka tura kuɗi, ka tabbatar cewa sunan Account ya fito daidai da NOVACHAIN ACADEMY LTD. Idan kuma zaka turawa ta OPay, ka tabbatar ka ga sunan NANA ISAH kafin ka kammala biyan kuɗin.
📲 BAYAN BIYA: A tura shaidar biyan kuɗi (receipt) ta WhatsApp zuwa:
07069591722
☎️ DOMIN ƘARIN BAYANI: Za ku iya kiranmu ta wannan lamba:
09135800666
NOVACHAIN BLOCKCHAIN ACADEMY
28/08/2026
3
130
Masha Allah❤
Sadiq Jega retweeted
WELCOME TO NOVACHAIN ACADEMY
Africa's Hub for Blockchain & Web3 Education, training the next generation of Blockchain & Web3 innovators.
The future belongs to those who understand emerging technologies.
NovaChain Blockchain Academy is dedicated to developing highly skilled Blockchain and Web3 professionals equipped to compete globally and contribute to Africa's digital transformation.
What We Teach
• Blockchain Technology
• Web3 Development
• Smart Contracts
• Decentralized Applications (DApps)
• Digital Assets
• Decentralized Finance (DeFi)
• Tokenomics
• Artificial Intelligence (AI)
• Digital Security
• Remote Work & Digital Entrepreneurship
Our programs combine practical training, real-world projects, continuous assessment, and professional certification to prepare students for the global digital economy.
Training Options
✔ Online Training (Worldwide)
✔ Physical Training (Abuja, Nigeria)
✔ Physical Training (Kebbi State)
✔ Corporate & Institutional Training
✔ Government & Institutional Training (Planned)
✔ Youth Empowerment Programs
Our Vision
To become Africa's leading center of excellence for Blockchain, Web3, and emerging technology education.
Our Mission
To empower individuals with practical digital skills that create opportunities, drive innovation, and prepare the next generation of digital professionals.
This is not a hype community. This is a learning community.
We sincerely appreciate your continued trust, support, and prayers for us.
To see the programs we have already introduced and those we will be presenting in the future, visit our Telegram channel:
t.me/NovaChainBA
Thank you to our community. 🙏
@KarrarCrypto
Founder, NovaChain Academy
27/08/2026
Alhamdulillah❤
OFFICIAL ANNOUNCEMENT 📢
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.
We would like to inform our entire community that we have changed the name of our Academy from NovaChain Blockchain Academy to NovaChain Academy. As you may have noticed, we have only removed the word “Blockchain” from the Academy’s name, while our mission, programs, and the vision for which NovaChain Academy was established remain unchanged.
Why did we change the name?
This change came as a result of some challenges we encountered while trying to register and obtain approval from certain authorities in Nigeria. The use of the word “Blockchain” in the Academy’s name resulted in additional scrutiny and made the approval process more difficult, particularly given the challenges faced by Blockchain and Crypto-related activities with regulatory authorities in Nigeria.
Therefore, in order to ensure that NovaChain Academy can operate properly, comply with regulatory requirements, and build a strong and sustainable educational institution, we considered it appropriate to make this adjustment.
All our programs and everything we have announced that we will teach remain exactly as planned. The name change is only intended to create a more effective administrative structure and increase our opportunities for collaboration with government authorities and other major organizations.
Our main goal is to build NovaChain Academy as a professional institution for modern education, while providing our students with quality knowledge and valuable Certificates of Completion.
We are also working to ensure that all our programs, our Certificate issuance system, and other important aspects of the Academy are structured in accordance with the relevant requirements of Nigerian authorities. This will further increase our opportunities to collaborate with various government authorities and organizations, while creating more opportunities for our students in the future.
Therefore, we call on our entire community and students to understand that only the name has changed, while our mission, programs, and vision remain unchanged.
We sincerely appreciate your continued trust, support, and prayers for us.
To see the programs we have already introduced and those we will be presenting in the future, visit our Telegram channel: t.me/NovaChainBA
Ja’afar Bala
Director General, NovaChain Academy
27/08/2026
2
4
103
Sadiq Jega retweeted
🚨 RANA TA BIYAR DA FARA REGISTRATION!
Alhamdulillah, yau mun shiga rana ta biyar da fara Registration na NovaChain Blockchain Academy.
A cikin kwanaki uku kacal, mun ga yadda mutane suka fara nuna sha’awa da fahimtar muhimmancin wannan shiri. Wannan ya tabbatar mana da abu ɗaya:
Lokaci yana canzawa, kuma wanda ya fara shirya kansa tun yanzu shi ne zai fi samun damar cin gajiyar abin da ke zuwa.
🌍 Duniya tana canzawa. Fasaha tana canzawa. Hanyoyin samun ilimi, aiki da kasuwanci suna canzawa.
Amma tambayar ita ce:
Kai fa, kana shirin canzawa tare da ita?
Blockchain ba wai Crypto Trading kawai ba ne.
A cikin shirin watanni 6 na NovaChain Blockchain Academy, za ka fara daga Basic, ka wuce Intermediate, sannan ka kai Advanced/Professional, inda za ka zurfafa fahimtar:
🔹 Blockchain & Web3
🔹 Digital Assets
🔹 Wallets & Exchanges
🔹 DeFi
🔹 Smart Contracts & DApps
🔹 Trading & Technical Analysis
🔹 Risk Management
🔹 P2P Trading
🔹 Blockchain Security
🔹 On-Chain Analysis
🔹 Web3 Development
🔹 AI & Web3
🔹 Digital Entrepreneurship
🔹 Practical Projects
🎯 ME YA SA KAKE JINKIRI?
Wataƙila kana cewa:
Zan fara daga baya.
Amma ka tuna: daga baya ba lokaci ba ne.
Idan ka ci gaba da cewa sai ka samu lokaci, sai ka samu kuɗi, sai ka shirya sosai, watakila ka ci gaba da kallon duniya tana tafiya ba tare da kai ba.
Ba sai ka zama ƙwararre kafin ka fara ba.
Abin da ake buƙata shi ne ka fara, sannan ka koyi yadda ake zama ƙwararre.
📚 Watanni shida na koyo na iya canza yadda kake kallon Blockchain, Web3 da Digital Assets gaba ɗaya.
📝 REGISTRATION NA CI GABA!
Registration Fee: ₦10,000
Kuɗin Karatu:
Basic — ₦2,000/wata
Intermediate — ₦3,000/wata
Advanced/Professional — ₦5,000/wata
💳 HANYAR BIYA
Name: NOVACHAIN ACADEMY LTD
Account: 6999531401
Bank: Moniepoint MFB
⚠️ Kafin ka biya, ka tabbatar sunan account ya kasance NOVACHAIN ACADEMY LTD.
📲 Bayan biya, a tura Proof of Payment ta WhatsApp:
09135800666
⏳ KAR KA JIRA SAI AN CE AN CIKA SLOTS.
Idan kana ganin wannan dama ta dace da kai, lokacin fara shiri shi ne yanzu.
NovaChain Blockchain Academy — Muna gina ƙarni mai fahimtar fasahar gaba.
NOVACHAIN BLOCKCHAIN ACADEMY
24/08/2026




















