BBC News Hausa (@bbchausa) header
BBC News Hausa (@bbchausa) profile picture

BBC Hausa - Fiye da shekara 60 na labaran duniya da rahotannin da suka shafi rayuwarku

London
Joined December 2008
Yadda Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sauka a Jeddah gabanin gudanar da ibadar Umrah a Makkah. Tinubu ya samu tarba daga Abdulaziz Yari da Abdussamad Rabiu da sauran ƴan Najeriya da jamiʼan Saudiyya. Tace hoto - Aminu Kutama
1
3
24
4,585
Tinubu ya tafi Saudiyya domin aikin Umara Ƙarin bayani - bbc.in/4zSqAPO
2
4
30
5,793
Soyayya ruwan zuma 💝 Wata matashiya ce soyayya ta ɗibe ta, ta haye saman hasumiyar sabis, kuma ta ce ba za ta sauko ba sai iyayenta sun ɗaura mata aure da saurayin da take so. Za ku iya wannan kasadar domin soyayya? #india #mumbai #soyayya #love
4
10
58
9,362
A rana irin ta yau, 29 ga watan Oktoba, shekara 20 ke nan da rasuwar marigayi Sarkin Musulmi na 19 a Najeriya, Alhaji Muhammadu Maccido, a wani hatsarin jirgin sama a shekarar 2006. Ƙarin bayani - bbc.in/4BA5hnZ
8
7
103
6,117
Shin me ya sa Tinubu ke ta ɓullo da sabbin tsare-tsaren rage raɗaɗi ga 'yan Najeriya? A baya-bayan nan, gwamnati ta gabatar da shirin bai wa ma'aikatan gwamnati tallafin 70,000 duk wata har tsawon wata shida, makonni bayan ta fitar da shirin tallafin rage farashin man fetur.
5
6
67
8,007
Nan gaba a yau ne hukumar zaɓen Najeriya, INEC za ta fitar da matsaya kan wasu ƴantakarar gwamna da ta cire sunayensu daga cikin jerin ƴantakara a zaɓen 2027 da ke tafe. Karain bayani - bbc.in/4e6kenF
3
12
1
231
14,708
A yayin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri’un zaɓen, Jam’iyyar Likud ta Firaminista Netanyahu, ta zargi jam’iyyun Larabawan ƙasar da maguɗin zaɓe ta hanyar cin hanci da razanarwa da amfani da tashin hankali. Ƙarin bayani - bbc.in/3Umf0O2
3
6
1
69
8,334
Kun san ana sayar da tsire da sauran abincin Hausawa a birnin London? Umar Bala, ɗan asalin Kano, ya bayyana yadda ya yi nasarar bunƙasa sana’ar sayar da abincin Hausawa a Ingila, inda ya fara a cikin ƙaramar mota har ta kai ga buɗe gidan abinci. 🎥 - Muhammadu Buhari Fagge
3
18
174
10,395
Daga sabuwar matatar tsaftace zinari da aka gina a Habasha zuwa wani katafaren aikin matatar mai na biliyoyin daloli a Kenya, ƙasashen Afirka suna ƙoƙarin samun ƙarin riba daga albarkatun ƙasashensu ta hanyar sarrafa su a cikin gida.
4
5
69
5,329
A daidai lokacin da mutanen Najeriya ke ƙara bayyana ra'ayoyinsu kan yanayin tattalin arzikin ƙasar, shugaban ƙasar ya ɓullo da wasu hanyoyi da matakai da ya ce za su rage raɗaɗin da ƴan ƙasar ke ciki. Ƙarin bayani - bbc.in/4zbjUMN
7
8
71
4,956
Masana yanayi na gargaɗin cewa Najeriya na iya fuskantar matsanancin zafi a watanni masu zuwa sakamakon tasirin yanayin El Niño, lamarin da ka iya haifar da matsalolin lafiya da muhalli ga miliyoyin mutane. Ƙarin bayani - bbc.in/3WbHGtC
3
3
40
3,792
Jadon Sancho ya ƙi amincewa da komawa gasar La Liga, yayin da Desire Doue ke tattaunawa da Paris St-Germain kan tsawaita kwantiraginsa. Ƙarin bayani - bbc.in/4ieY7hi
3
46
3,069
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wannan tafiya za ta bai wa shugaban ƙasar damar gudanar da ayyukan ibada da kuma yi wa Najeriya addu'o'in samun zaman lafiya. Ƙarin bayani - bbc.in/3UQy2w8
41
15
3
229
12,980
A zamanin wane shugaba ne ‘yan Najeriya suka fi fama da talauci? Bola Ahmed Tinubu ya ce matsalolin yunwa da talauci da ake gani yanzu sun samo asali ne daga matsalolin da gwamnatocin baya suka bari. To amma mun binciko muku abin da alƙaluman Bankin Duniya suka ce.
36
25
2
256
20,751
Wadanne ƙasashen Afirka ne tattalin arzikinsu ke bunƙasa cikin sauri? 🌍 A cewar hasashen baya-bayan nan na Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), wasu daga cikin ƙasashen Afirka na daga cikin ƙasashen da tattalin arzikinsu ke bunƙasa. Ga dalilin da ya sa hakan ke faruwa.
7
9
151
12,104
Hatsarin ya shafi wani jirgin ƙasa da ya tashi daga Madrid zuwa Seville da kuma wani jirgin da rahotanni suka ce yana tsaye cak a lokacin da lamarin ya faru. Ƙarin bayani - bbc.in/4jKyZjN
1
53
7,551
Kylian Mbappe ya jefa kansa da La Liga cikin wata matsala a China bayan da wasu ‘yan kasar ke fushi da shi saboda ya kira tsohon shugaban kasar Mao Zedong Mai mulkin kama karya, a wani yanayi na wasa. 🎥 - Abdulrazzaq Kumo
3
15
244
16,009
Tallafin na zuwa ne a lokacin da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa ke ci gaba da ƙara wa ma'aikata da iyalansu nauyi Ƙarin bayani - bbc.in/4klGoGg
6
8
3
133
9,650
A wannan karon Larabawan Isra'ila, waɗanda galibi ke bayyana kansu a matsayin 'yan Isra'ila masu asalin Falasɗinawa waɗanda yawansu ya kai kashi ɗaya cikin biyar na al'ummar ƙasar, sun yi irin fitowar da ba su taɓa yin irin ta ba a baya. Ƙarin bayani: bbc.in/4zYxTFQ
9
1
163
9,200
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya ce yana girmama Nasir El-Rufai kamar yadda yake girmama duk tsoffin gwamnonin jihar Kaduna. Ya bayyana hakan ne yayin da El-Rufai ke tsare a hannun hukumomi, bayan da wasu ke zargin gwamnan da yi masa butulci.
27
9
5
205
11,457